Sabuwar wallafa: Rubuce-rubucen al-Hajj Musa Ibn Hissein, wani masani daga Barno (Nijar, Nijeriya)

Par Ari Awagana et Camille Lefebvre

A shekara ta 1904 wasu masana guda biyu suka haɗu a masallacin al-Azhar da ke birnin Alƙahira: wani malami daga Barno mai suna al-Hajj Musa da wani masanin ilimin harsuna daga Jamus, Rudolf Prietze. Dukansu biyu sun kasance a Masar ne don su ci gaba da karatunsu. Suka yi haɗin gwiwa na nazari tsawon shekaru goma, suka samar da ɗaruruwan shafuka na rubutu a cikin harshen Kanuri. Duk da haka, da zarar masanin ilimin harsunan nan ya koma Turai, ya buga takardun nan duka a sunansa shi kaɗai. Al-Hajj Musa ya ɓace daga wannan labari; rubuce-rubucen da aka tattara ba su da marubuci ke nan.

Shekaru 120 bayan haka, Ari Awagana da Camille Lefebvre suka yi bibiya suka bincika haɗuwar nan da ta haifar da wannan aiki na haɗin gwiwa, don su gano yanayin da waɗannan mutane biyu suka yi aikin tare.
Abin da aka gabatar a matsayin aikin Bature, a haƙiƙance haɗin gwiwa ne na ilimi wanda yake da mafarinsa a cikin ayyukan nazarce-nazarce na ilimin harsuna a Jamus na ƙarshen ƙarni na 19 da kuma adabin baka na Sahel ta tsakiya. Haɗuwar malaman nan guda biyu ce ta haifar da wannan aikin haɗin gwiwa.

A yau, Ari Awagana da Camille Lefebvre suka sake buga duk waɗannan matanai na harshen Kanuri waɗanda suka ƙunshi waƙoƙi, karin magana, wasiƙu, labaran tarihi, a cikin juzu’in rubutu biyu, guda na ƙarni na 19, guda kuma a sabuwar ƙa’idar rubutun Kanuri ta yanzu wadda masu magana na zamani za su iya karantawa, suka kuma fassara su zuwa Faransanci don su isa ga mafi yawan jama’a. An buga wannan littafin ne da kuɗaɗe daga Hukumar Bincike na Tarayyar Turai (ERC) mai suna [Horizon 2020 Research and Innovation Programme], GA No. 759390, wanda ke ba mu damar sauke shi gaba ɗaya a kyauta a wannan hanyar haɗin yanar gizon.


OpenEdition vous propose de citer ce billet de la manière suivante :
awagana (3 juillet 2025). Sabuwar wallafa: Rubuce-rubucen al-Hajj Musa Ibn Hissein, wani masani daga Barno (Nijar, Nijeriya). Langarchiv. Consulté le 11 février 2026 à l’adresse https://doi.org/10.58079/149pv


Laisser un commentaire

Votre adresse e-mail ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.